Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Alamar Tambaya Game Da Zaben Gabon In Ji Masu Sa Ido


 Ali Bongo
Ali Bongo

Masu saka ido na Kungiyar Tarayyar Turai a kasar Gabon sun ce akwai rashin daidaito karara a sakamakon zaben da ya nuna cewa da kyar Shugaba Ali Bongo ya yi galaba akan abokin karawarsa Jean Ping.

Masu saka idon na kungiyar Tarayyar Turai ta EU da ke Gabon na jefa ayar tambaya akan sakamakon da ya fito daga lardin Upper Ogooue, inda Mr. Bongo ke da tasiri, inda a hukumance ya lashe kashi 95% na kuri'un

Sakamakon zaben yankin ya nuna cewa kashi 99% na masu kada kuri'a ne su ka fito.

Bangaren adawa ya ce an yi kari sosai kan ainihin adadin kuri'un wannan lardin.

A wani bayani jiya Talata, tawagar ta EU ta lura cewa an fuskanci rashin fitowar masu kada kuri'a sosai a sauran larduna takwas na Gabon, wanda ya nuna cewa kimanin masu kada kuri'a 48% ne su ka fito a fadin kasar.

Shugaban masu saka idon na EU, ya jaddada kiraye-kiraye ga hukumomin Gabon da su wallafa sakamakon kowace mazabar da ke kasar.

A jiya Talata Firai ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce ya kamata kasar ta Gabon ta sake kidaya kuri'un, bayan da bangaren adawa ya yi zargin cewa an tafka magu.

A makon jiya Hukumar Zaben Gabon ta ayyana Shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya yi galaba kan jagoran 'yan adawa Jean Ping da kuri'u kimanin 5,000, lamarin da ya janyo zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar mutane 6.

Ministan Shari'ar Gabon, Seraphin Moundounga, ya yi murabus saboda takaddamar da ake yi kan zaben na Gabon, shi ne kuma babban jami'in gwamnati na farko da ya yi murabus tun bayan zaben.

XS
SM
MD
LG