Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Jan Aiki  A Gaba – Kocin Manchester United Rangnick


Ralf Rangnick (AP)

A minti na 82 dan wasan Wolverhampton Joao Moutinho ya zura kwallo a ragar United a wasan da suka kara a gasar Premier League wanda aka tashi 1-0.

Mai horar da ‘yan wasan Manchseter United Ralf Rangnick, ya ce akwai jan aiki a gaba muddin kungiyar na so ta yi zarra a nan gaba.

Ranganick ya bayana hakan ne bayan kayen da United ta sha hannun Wolverhampton da ci daya mai ban haushi.

Wannan shi ne kaye na farko da kungiyar ta fuskanta karkashin sabon kocin dan asalin kasar Jamus.

A karshen watan Nuwamba aka nada Rangnick a matsayin kocin wucin gadi bayan da aka sallami Ole Gunner Solskjaer.

“Ko kadan ba mu taka rawar a zo a gani ba, wannan wasa ya nuna cewa muna da aiki babba a gabanmu da za mu yi.” Ranganick ya ce kamar yadda AP ya ruwaito.

A minti na 82 dan wasan Wolverhampton Joao Moutinho ya zura kwallo a ragar United a wasan da suka kara a gasar Premier League.

Dubi ra’ayoyi

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

AFCON 2021, Ahmed MusaQueiroz ta Masar

Queiroz ta Masar, "Ba mu kasance cikin filin wasa ba a farkon rabin lokaci 'yayin da' Najeriya ta ci nasara''
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Najeriya na atisaye gabanin wasanta na farko da Masar a rukunin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG