Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ta Tafka Muhawara Kan Kayen Da Manchester United Ta Sha A Hannun Villa 


Bayan da Bruno ya zebra da fenariti
Bayan da Bruno ya zebra da fenariti

Rabon da Aston Villa ta doke Manchester United tun a watan Disambar shekarar 2009 a wasan da suka hadu a Old Trafford.

Masoyan kungiyar Manchester United a sassan duniya na ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta muamman a Twitter kan barar da fenariti da Bruno Fernandes ya yi a wasansu da Aston Villa.

Villa ta bi Manchester United har Old Trafford ta doke ta da ci 1-0.

Mai tsaron gidan Villa Kortney Hause ne ya zama zakaran wasan bayan da ya yi amfani da kansa ya zura kwallo a ragar David De Gea a minti na 88.

Rabon da Villa ta doke United tun a shekarar 2009.

Amma a minti na 90+5, United ta samu bugun fenariti bayan da Hause ya taba kwallon da hannunsa.

'Yan wasan Villa suna taya Hause, dama murnar kwallon da ya ci
'Yan wasan Villa suna taya Hause, dama murnar kwallon da ya ci

Sai dai Bruno wanda ya buga fenaritin ya zubar, inda ya doka kwallon ta tashi saman ragar Villa.

Hakan ya sa aka ta shi a wasan da ci 1-0.

Wannan nasara da Villa ta samu akan Manchester United bai yi wa masoyan United dadi ba lamarin da ya haifar da muhawara a shafukan sada zumunta.

Yayin da wa suke dora laifin akan Bruno da ya zubar da fenaritin wasu kuwa suna dora laifin ne akan rashin hadin kan ‘yan wasan na United.

“Sun nuna son kai a wasan, babu hadin kai, ya kamata a canja Ole, Man U na bukatar kocin da zai iya raya mashahuran ‘yan wasan.” In ji @Miky50326508.

Kocin United Ole Gunnar Solskjaer
Kocin United Ole Gunnar Solskjaer

“Greenwood da Bruno kwallon son kai suka buga, kowannensu yana so a ce shi ne zakaran wasan, sun manta cewa suna wasan ne a matsayin kungiya, abin kunya.” In ji @lamamamam.

“Ronaldo ya ji tsoron buga fenaritin, ba zai iya da nauyin da ya rataya a wuyansa na buga fenaritin a wannan lokaci ba.” @rentfreeiyh ya ce.

“Tsoro ba mahadin Ronaldo ba ne, abin da ka fada ba ma’ana.” @Mischief Ronnie ya mayarwa da @rentfreeiyh martani.

Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?

Ole Gunnar Solskjaer
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG