Ayukan ba da agaji na neman yin karanci ga kusan mutane miliyan daya da suka arce wa tashin hankali a baya bayan nan a arewa maso yammacin Syria, a cewar shugaban ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya kuma jaddada kiran tsagaita wuta.
Babban jami'in a fannin bada agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Marl Lowcock ya bayyana hakan ne bayan da shi da wasu jami’an majalisar suka dudduba wasu kayayyakin tallafi akan iyakar Turkiyya da gundumar Idlib dake Syria.
Ya ce majalisar ta gano cewa mutane na zama cikin fargabar harin bama-bamai da tashin hankali, kuma suna matukar bukatar matsugunni, abinci, tsabta, kiwon lafiya da kuma tsaro.
Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Kelly Craft ne dan rakiyar Lowcock, wanda ya ba da sanarwar karin tallafin Amurka na dala miliyan 108 ga ayukan tallafin.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 18, 2021
Kungiyar Kasuwanci ta Duniya Na Bukatar Sabon Salon Gudanarwa-Dr. Ngozi
-
Fabrairu 18, 2021
Guterres Ya Yi Kiran a Samar Da Tsarin Bai Daya Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 16, 2021
Kungiyar WTO Ta Gabatar Da Sabuwar Shugaba Ngozi Okonjo-Iweala
-
Fabrairu 16, 2021
Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Aminta Da Riga Kafin AstraZeneca