Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Rarrabuwar Ra'ayi kan Cigaban Najeriya a Shekaru 57 da Samun 'Yancin Kai


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Akwai rarrabuwan ra'ayi kan irin cigaban da Najeriya ta samu cikin shekaru hamsin da bakwai da samun 'yancin kai daga turawan Ingila

Shekaru 57 da samun 'yancin kan Najeriya wasu na ganin an samu cigaba yayinda wasu ke kallon cigaban zaman irin na mai hakan rijiya musamman ta bangaren tattalin arziki.

Duk da yake Allah ya huwacewa kasar albarkatu masu dimbin yawa masana tattalin arziki na cewa kasar na fuskantar koma baya ta hanyar tattalin arzikin idan aka kwatantata da sauran kasashe takwarorinta a fadin duniya.

Bashir Muhammad Acida malami a sashen ilimin tsimi da tanadi na Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto na mai cewa "abubuwa sun tabarbare tun lokacin da aka gano mai. Idan aka duba duk kasashen duniya inda aka gano mai sun cigaba saidai masu mulki mai yanayi irin namu. Amma mu lokacin da muka gano mai sai muka yi watsi da abun da ya taimakawa noma da sauransu. Mun bar wasu abubuwa. Mun bar ilimi kuma idan ka bar ilimi baya dole a samu matsala"

Ya cigaba da cewa kasar tana baya saboda tabarbarewar ilimi fiye da yadda ake zato. Yace da can da babu mutane da yawa abu kadan sai ya isa amma ba haka lamarin yake ba yanzu. Da can kowa na dogaro ga kansa ba kamar yanzu ba da kowa ya mai da hankali ga gwamnati, inji Bashir.

Tsohon ministan kudi na Najeriya Alhaji Abubakar Alhaji ya koka da halin da kasar ke ciki yanzu musamman idan aka yi la'akari da cewa kasar ta taba ba asusun lamuni na duniya IMF rancen kudi a shekarar 1974. Shi da kansa ya rabtaba hannu akan rancen.

Saidai Farfasa Bello Bada mai sharhi akan alamuran yau da kullum na Jami'ar Usmanu Dan Fodio ta Sokoto ya bayyana dalilin sauyawar alamura.Yana mai cewa a lokacin gidaje nawa ne shugaban kasar ya mallaka. Gwamnoni nawa ne kuma gidaje nawa suka mallaka? Nawa suke dashi a waje? Amma yanzu bayan mutum ya yi shugaban kasa sai a ga ya mallaki makudan kudi a ciki da wajen kasar. Ya cigaba da cewa mutane sun wawure dukiyar kasar sun barta da zuwa neman bashi.

Mafta daya ce inji Farfasa Bashir a koma ga kishin kasa a kuma yaki cin hanci da rashawa da gasken gaske.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG