Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al Bashir Ya Ajiye Shugabancin Jam'iyyarsa Ta NCP


shugaban Sudan, Omar Al Bashir yayin wani jawabi da ya yi a ranar 22 ga watan Fabrairu daga fadar shugaban kasa

Shugaban Sudan, Omar Al Bashir, ya sauka daga mukaminsa na shugaban jam’iyyarsa da ke mulkin kasar.

Jam’iyyar National Congress Party, wacce ake kira NCP takaice, ta fitar da wannan sanarwa a karshen makon nan ne, bayan da aka kwashe makonni ana zanga zangar nuna adawa ga gwamnatin Al Bashir.

Yanzu haka, shugaban na Sudan ya mika mukamin ga mataimakinsa, Ahmed Harun, har sai zuwa lokacin babban taron da jam’iyyar za ta yi a nan gaba, inda a lokacin ne za ta zabi sabon shugaba.

Amma dai ba a saka ranar da za a gudanar da babban taron ba.

Ita dai jam’iyyar ta NCP, ita ke morar rinjaye a majalisar dokokin kasar, kuma bisa wata matsaya da aka cimma a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar, shugaban jam’iyya shi ke zama dan takararta a zaben shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG