Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al Hassan Ya Ki Bai Wa Jami'an Tsaro Hadin Kai


Al Hassan Ag Abdoul Aziz
Al Hassan Ag Abdoul Aziz

Wani da ake zargin cewa dan kungiyar Islama ne wanda aka kama a kasar Mali ya ki hada kai da jami'an tsaro domin a masa sassaucin hukunci yayin da lauyoyinsa suka jaddada cewa bai da koshin lafiyar da zai tsaya a yi shari'a.

An kama Al Hassan Ag Abdoul Aziz ne a shekarar 2018 a Mali inda aka ce yana daya daga cikin kusoshin rudunar Ansar Dine, wata kungiyar ‘yan bindiga da ta yi mulkin arewacin Mali kusan na shekara guda a 2012.

Al Hassan Ag Abdoul Aziz
Al Hassan Ag Abdoul Aziz

Masu gabatar da karar na zargin Al Hassan da haddasa laifuka da dama, da suka hada da azabtarwa, fyade, cin zarafi da sauran munanan laifuka.

Babban mai gabatar da kara a kotun ta ICC, Fatou Bensouda ta ce ana kuma zargin Al Hassan na daga cikin wadanda suka lalata wurare da kayayyakin tarihi kamar gumaka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG