Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al-Qaida ta Ayyana Kasar Iraqi Mai Bin Tafarkin Islama


Titunan birnin Falujjah shal, kuma za a ga konannun motoci.
Titunan birnin Falujjah shal, kuma za a ga konannun motoci.

A Iraqi mayakan sakai na al-Qaida sun ayyana kasa mai cikin gashin kai dake tafarkin shari’a, bayan da suka kama birnin Fallujah mai fama da fitintinu dake yammacin kasar.

A Iraqi mayakan sakai na al-Qaida sun ayyana kasa mai cikin gashin kai dake tafarkin shari’a, bayan da suka kama birnin Fallujah mai fama da fitintinu dake yammacin kasar jiya jumma’a. Saye da bakaken tufafi mayakan sun aza tutocinsu kan gine gine gwamnati dake yankin.

Shaidun gani da ido sun ce mayakan sakan ‘yan kungiyar da take kiran kanta kasar Iraqi da Syria masu bin tafarkin Islama, ko ISIS a takaice, sun yanke wutan lantarki a birnin suka kuma umarci mazauna yankin kada su yi amfani da janareta.

Amma baturen ‘Yansanda na binrin Fallujah Mohammed al-Isawi, ya karyata ikirarin mayakan cewa su suke rike da birnin, a hira da jaridar New York Times, baturen ‘Yansandan yace ya girke jami’ans a daga arewacin birnin domin shirin karon batta.

Yace dakarunsa sun sami goyon bayan shugabannin kabilu, kuma tuni har sun kwace wani bangaren birnin a daren jiya.

Wani dan jarida a kasar wanda ya nemi a sakaye sunansa ya gayawa jaridar Washington Post cewa ‘Yansanda da wasu jami’an gwamnati duk sun gudu, kuma ‘yan al-Qaidan sun kona duk tutocin Iraqi.

Fada da ake gwabzawa a yammacin kasar ya zamo zakaran gwajin dafin karfin PM kasar Nouri al-Maliki na ci gaba da hade kan kasar lamari d a zai hana barkewar yakin basasa gadan gadan.
TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG