Accessibility links

Jami'an Tsaron Amurka Sun Kama Abu Anas al-Liby

  • Halima Djimrao

Irin wadanda hukumomin Amurka ke nema ruwa a jallo

Ana zargin Abu Anas al-Liby da hannu a hare-haren boma-boman shekarar 1998 a ofisohin jakadancin Amurka na Kenya da Tanzania

Jami'an gwamnatin Amurka sun ce sojojin kasar sun kama wani shugaban al-Qaida da ke fuskantar tuhuma daga gwamnatin Amurka saboda hare-haren boma-boman shekarar Alif Dari Tara da Casa'in da Takwas da aka kaiwa ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Kenya da Tanzania.

Jami'ai sun ce mutumin da ake zargin, sunan shi Abu Anas el-Liby, kuma ranar asabar aka kama shi da ran shi a kusa da birnin Tripoli,a ksar Libiya cikin wani samamen hadin guiwar sojojin Amurka da jami'an leken asirin kasar.

Amurka ta yi bayanin samamen da ta kai ne jim kadan bayan da 'yan uwan Abu Anas dan shekaru Arba'in da Tara suka fara cewa an sace shi a birnin Tripoli.

Kamfanin dillancin Labaran Reuters ya ruwaito wani dan uwan shi ya na cewa an tafi da Abu Anas a lokacin da yake ajiye motar shi a kofar gidan shi da jijjifin asabar bayan sallar asuba. Ya ce wasu motoci uku suka zagaye shi, su ka fasa gilashin tagar motar shi, suka kwace makamin da yake dauke da shi sannan suka gudu da shi.
XS
SM
MD
LG