Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al Shabab Ta Dauki Alhakin Harin Mogadishu


Masu ayyukan ceto suna kokarin ba da agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata a harin da aka kai a Mogadishu, ranar 4 ga watan Febrairu

Masu kamfanin rukunin motocin jigilar majinyata na Aamin sun fada wa ‘yan jarida cewa sun dauko gawarwaki a kalla 9, ciki har da na wasu mata uku.

Kungiyar mayaka ta al-Shabab mai tsattsauran ra’ayin addini ta yi ikirarin kai wasu hare-hare biyu a Somalia jiya Litini, inda mutane akalla 9 su ka mutu.

An kai harin ne da bam da aka saka a cikin mota a tsakiyar birnin Mogadishu, sannan kuma aka harbe wani mutum a wata tashar jirgin ruwa a yankin Puntland mai kwarya-kwaryar ‘yancin cin gashin kai.

Masu kamfanin rukunin motocin jigilar majinyata na Aamin sun fada wa ‘yan jarida cewa sun dauko gawarwaki a kalla 9, ciki har da na wasu mata uku.

Sannan sun yi jigilar wasu mutane 7 da su ka ji raunuka. Haka zalika, wasu majiyoyin tsaro sun gaya ma Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa an hallaka wani babban jami’in tsaro a wannan harin.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG