Gwamnan jihar Agadez ya isa wurin da lamarin ya faru kuma ya je babban asibitin jihar domin ganin halin da wadanda suka jikkata suke ciki.
Madame Hajiya Alzuma, ita ce mataimakiyar magatakardan gwamnan jihar Agadez, a lokacin ziyarar ta bayyana yadda lamarin ya faru.
Adamu Hudu, malamin yaran almajiran da wannan ittila'in ya rutsa da su ya ce karar da ji ta sa ya fita waje ya ga yaran a cikin mummunan yanayi.
Jami’an kwana - kwana su ne su ka kai agaji a lokacin da wannan abu ya faru kuma shugaban su Lieutenant Taro Mahamadu ya ce bututun iskar gas na dafuwa ne ya fashe,
Haka kuma hukumomi sun tabbatar da cewa ba bom ne ba kuma ba wani makamin yaki bane.
Ga karin bayani cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 26, 2021
An Kama Makamai a Jihar Tahoua a Nijar
-
Janairu 25, 2021
'Yan Ta'adda Sun Kashe Sojoji A Kasar Mali Tare Da Jikata Wasu
-
Janairu 24, 2021
An Kashe Mayakn Al-Shabab 189 A Wani Samame Da Aka Kai A Mabuyar Su
-
Janairu 23, 2021
An Kama Wani Direban Motar Asibiti Dauke Da Lodin Tabar Wiwi a Nijer
-
Janairu 18, 2021
'Yan Adawa A Uganda Sun Ki Yarda Da Sakamakon Zaben Ranar Lahadi
Facebook Forum