Accessibility links

al-Shabab Ta Hallaka 'Yan Sanda 15 A Somaliya

  • Ibrahim Garba

Wasu dakarun al-Shabab

Kungiyar Ta'addar al-Shabab ta sake kai wani mummunan hari na ba-zata a Somaliya, kuma ana jayayya kan adadin wadanda abin ya rutsa da su - musamman daga bangaren sojin kasar.

An hallaka 'yan sandan Somaliya akalla 15 a wani farmakin da aka kai wurin duba ababen hawa a Afgoye, mai tazarar kilomita 30, kudu maso yammacin birnin Mogadishu, a cewar jami'ai.

Gwamnan Shabelle ta Kasa Abdulkadir Mohammed Nur Sidi ya gaya ma Muryar Amurka cewa wasu mayakan al-Shabab ne dauke da muggan makamai su ka kai hari kan wurin duba ababen hawan cikin dare, su ka kama wurin na wani dan lokaci, to amma da safiyar jiya Asabar jami'an tsaro su ka fatattake su.

"Sun tafi da motoci biyar na 'yan sanda, to amma jami'an tsaro sun bi sawu sun kwato guda," in ji shi.

Wata majiya ta gaya ma Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa an kashe sojojin Somaliya sama da 10 a fadan. To amma gwamnan ya ki tanatance adadin; saidai ya ce an hallaka mayakan al-Shabab fiye da 30 a hare-haren biyu.

XS
SM
MD
LG