Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

al-Shabab ta kai hari a Mogadishu Akalla Mutane Biyu Sun Halaka.


Sansanin wani O'tel da al-Shabab ta kaiwa hari a baya.

Kungiyar ta kai harin ne a harabar wani gidan cin abinci mai farin jini ga farar hula da jami'an tsaro duka.

Wani harin bam da aka kai cikin wata mota da aka auna kan jami'an tsaro a Mogadishu babban birnin kasar ya halaka akalla mutane biyu ya jikkata wasu shida, kamar yadda bayanai da aka samu daga jami'an tsaron kasar suka nuna.

Yau Asabar ne aka kai harin a harabar wani gidan cin abinci da ake kira Blue Sky.
Farar hula da jami'an tsaron kasar wadanda suke aiki a wani gidan furisna dake karkashin kulawar hukumomin leken asirin kasar, wanda bashi da nisa da wurin cin abinci duka suna zuwa wurin.

Jim kadan bayan harin ne kungiyar al-shabab mai alaka da al-Qaida ta fiddsa sanarwa a wata kafar ada zumunta ta dauki alhakin kai harin, tana mai cewa ta auna harin ne kan jami'an tsaron jami'an tsaron dake aiki a gidan yarin.

Wani jami'in tsaron kasar ya gaywwa Sashen Somalia na MA cewa an kai harin ne da wata farar mota kirar Toyota Corolla wacce aka dankarawa nakiyoyi kaum aka tada su a gaban gidan cin abincin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG