Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'umma Na Da 'Yancin Sanin 'Yan Canji Dake Daukar Nauyin Boko Haram-MBF


Wasu mayaan Boko Haram/ISWAP da suka mika wuya da makamai (Facebook/Dakarun Najeriya).

Kungiyar al’ummomin dake jihohin tsakiyar Najeriya wato Middle Belt Forum ta kalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayan wadanda ke tallafawa kungiyar Boko Haram.

Kungiyar ta bayyana a wani taro da ta yi cewa, akwai butakar bayyanawa 'yan Najeriya mutanen da aka ce suna kara hasasa matsalar tsaro musamman masu mu’amala da kudaden ketare su dari hudu da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta zarga.

Kakakin kungiyar ta Middle Belt Forum, Dakta Isuwa Dogo yace taron ya tattauna batutuwan tsaro ne musamman a jihohin shiyyar tsakiyar Najeriya.

Shima shugaban kungiyar kananan kabilu a Arewacin Najeriya, Suleiman Sukukum yace hakkin gwamnati ne ta kare ‘yan kasa, amma idan ta gaza yin hakan, ya zamo dole mutane su nemi hanyoyin tsare kansu bisa ka’idar doka.

Kungiyar ta Middle Belt Forum ta kuma bukaci a samar da hukuma ta musamman da zata raya yankin da kawo karshen matsalolin tsaro a jihohin dake tsakiyar Najeriya.

Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti:

Kungiyar middle belt kan matsalar tsaro-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG