Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mayakan Boko Haram Dubu Biyar Ne Suka Mika Wuya - Sojojin Najeriya


Wasu 'Yan Boko Haram da suka yi saranda (Facebook/Dakarun Najeriya)
Wasu 'Yan Boko Haram da suka yi saranda (Facebook/Dakarun Najeriya)

Mayakan sun mika kansu ne ga rundunar Operation Hadin Kai OPHDK  a shiyyar Arewa Maso Gabashin kasar.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai, mukaddashin Darektan cibiyarsamar da bayanai na hedkwatar tsaron Najeriya Brigadier General Bearnad Onyeako ya ce kimanin ’yan Boko Haram dubu biyar da dari takwas da casa'in ne suka yi saranda tare da mika wuya ga dakarun Najeriya

Mayakan sun mika kansu ne ga rundunar Operation Gadin Kai OPHDK a shiyyar Arewa Maso Gabashin kasar.

Cikin Wannan adadi, Janar Onyeako ya ce akwai kwamandoji da mayakan naBoko Haram da suka hada da manyan kwamandoji guda Uku, Amir Amir guda hudu da Na’ibai guda biyar da kuma wasu da suka kware wajen satar shanu ma Boko Haram din da ma sauran gama garin ‘yan kungiyar din da iyalansu.

Hedkatar Tsaron Najeriyar ta ce tuni sojoji sun mika wani bangare na Boko Haram da suka yi saranda ga gwamnatin jihar Borno.

Janar Faruk Yahaya (a gaba)
Janar Faruk Yahaya (a gaba)

Tuni dai Hukumar wayar da kan jama'a ta Najeriya ta ce wannan saranda da ‘yan Boko Haram din ke ta yi wani ma'auni ne dake nuna irin nasara da jami'an tsaron Najeriya ke samu a yaki da ta'addanci kamar yadda Darakta Janar na hukumar Dr. Garba Abari ke cewa wannan babban abin farin ciki ne

Ana kan batun wannan saranda ne kuma wasu bijirarrun mayakan Boko Haram din suka yi arangama da sojoji inda suka lallasasu da ma kasha kimanin ‘yan ta'addan guda arba'in da cafke guda ashirin da kuma kone sansanin adana kayan fada da ma motocin yakin Boko Haram din guda uku.

Wata motar mayakan Boko Haram da sojoji suka kona (Facebook/Sojojin Najeriya)
Wata motar mayakan Boko Haram da sojoji suka kona (Facebook/Sojojin Najeriya)

Janaral Onyeako ya ce sojojin sun kuma kwato bindigogi da harsasai na AK47 sama da dubu biyu da bindigogin harbo jiragen sama da dai sauran kayan fada daga yan ta'addan Boko Haram din yayin wannan gumurzu.

XS
SM
MD
LG