Accessibility links

Al'ummar Garin Baga A Jihar Borno Sun Ce Da Walakin


Mutanen garin Baga sun taru su na kallon irin barnar da aka yi musu a bayan fadan da aka gwabza a garin tsakanin sojoji da 'yan bindiga

Mazauna garin sun ce har yanzu su na cikin tasku, kwanaki biyar a bayan fadan da ya janyo mutuwar daruruwan mutane tare da kona kimanin rabin garin

Mutanen garin Baga dake bakin tabkin Chadi kusa da iyakar Najeriya da Chadi, sun ce har yanzu su na cikin tasku, a saboda jami'an tsaro ba su bar 'yan agaji sun fara shiga garin ba sai dazu da rana a yau laraba.

An kona kusan rabin wannan gari, yayin da mutane masu yawan gaske suka rasa rayukansu a fadan da sojojin Najeriya suka ce sun gwabza da 'yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan kungiyar nance da aka fi sani da sunan Boko Haram.

Amma a wani lamarin da yaso yayi kama da abinda ya faru a tsakanin sojojin na Najeriya da mutanen garin Zaki-Biam a Jihar Binuwai a zamanin gwamnatin Obasanjo, an fara kukar cewa sojojin sun wuce gona da iri wajen kai farmaki da gangan a kan gidajen fararen hula.

A yanzu haka ma, shi kansa shugaba Goodluck Jonathan ya kafa hukumar binciken abubuwan da suka faru a garin Baga, haka ma majalisar dokokin tarayya ta Najeriya da ita kanta gwamnatin Jihar Borno.

Ga hirar wani mazaunin garin na Baga da Muryar Amurka kan abubuwan da suke wakana yau laraba a garin na Baga.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG