Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alassane Quattara Zai Sake Tsayawa Takarar Shugaban Kasar Ivory Coast


A mako mai zuwa ake sa ran Shugaban Ivory Coast, Alassane Quattara zai bayyana matsayarsa kan sake tsayawa takarar shugaban kasar.

Ana sa ran zai bayyana matsayar tasa ne a wani jawabi da aka shirya zai yi wa al’umar Ivory coast a ranar shida ga watan Agusta.

Jam’iyyar RHDP mai mulki a kasar ta Ivory Coast ta zabi Ouattara don ya sake neman mukamin shugaban kasa a karo na uku, amma kuma bai ce uffan ba kan wannan tayi da aka masa na neman yin tazarce.

A farkon shekarar nan, Ouattara mai shekara 76 ya bayyana shirinsa na mika mulki ga sabbin jini.

Amma ana ganin mai yiwuwa ya sake shawara bayan mutuwar Firai Ministansa Amadou Gon Coulibaly, wanda shi ya so ya gaje shi.

A farkon watan nan Firai Minista Coulibaly ya rasu sanadiyyar matsalar bugun zuciya

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG