Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alex Iwobi Ya Warke Daga Cutar Korona, Zai Buga Wasan Najeriya Da Lesotho


Alex Iwobi (Hoto: Instagram Alex Iwobi)

Dan wasan Super Eagles Alex Iwobi, ya warke daga cutar coronavirus da aka gano ya kamu da ita gabanin wasansu da Benin a Porto Novo.

“Hukumar kwallon kafa ta CAF, ta sahale Alex Iwobi ya buga wasansu da Lesotho” Shafin Super Eagle na Twitter ya wallafa ranar Talata.

An gano cewa Iwobi yana dauke da cutar ne, a lokacin da aka yi wa ‘yan wasan Najeriya gwajin cutar gabanin wasansu da Jamhuriyar Benin a ranar Asabar.

“Amma gwaje-gwajen baya-bayan nan da aka yi masa, sun nuna cewa ya rabu da cutar. Dakin binciken cututtuka na Clina Lancet da ke Legas ne ya gudanar da gwajin. Hakan na nufin, Iwobi zai buga wasan na yau.” In ji hukumar ta Super Eagles.

Wani hoton bidiyo da shafin na Super Eagles ya wallafa, ya nuna dan wasan na Everton, yana mika godiyarsa.

“Ya zama dole na bi ka’idojin da hukumar kwallon kafa ta FIFA da CAF suka gindiya, inda na kebe kaina a daki.”

“Ina godiya ga dukkan wadanda suka nuna min kauna, musamman shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, da abokan wasana.”

Tsohon dan wasan na Arsenal, ya ce bai ji alamun cutar sosai ba, abin da ya sa bai galabaita ba.

Najeriya, wacce ta riga ta samu gurbi, na shirin karawa da kasar Lesotho a yau, a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da za a yi a Kamaru.

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

AFCON 2021, Ahmed MusaQueiroz ta Masar

Queiroz ta Masar, "Ba mu kasance cikin filin wasa ba a farkon rabin lokaci 'yayin da' Najeriya ta ci nasara''
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:52 0:00
Karin bayani akan AFCON 2021

AFCON 2021, Super Eagles

Najeriya na atisaye gabanin wasanta na farko da Masar a rukunin D na gasar AFCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:54 0:00
Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG