Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Najeriya Ta Samu Gurbin Shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka


'Yan wasan Najeriya (Hoto: Twitter Super Eagles)
'Yan wasan Najeriya (Hoto: Twitter Super Eagles)

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya, sun samu damar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON, wacce za a yi a Kamaru a bana.

Najeriyar ta samu wannan damar ce bayan da ta doke Jamhuriyar Benin da ci daya mai ban haushi a filin wasa na Charles de Gaulle Porto Novo da ke kasar ta Benin mai makwabtaka da Najeriyar.

Ko da yake, tun kafin buga wannan wasa, Najeriya ta samu gurbinta saboda ‘yan wasan Saliyo sun tashi canjaras da Lesotho a wasan da su ma suka buga a ranar Asabar.

Dan wasan Najeriya Paul Onuacho ne ya zurawa Najeriya kwallonta cikin minti na 93.

Onuacho ya shiga wasan ne a matsayin dan canji.

Najeriya dai ita ta mamaye zagayen farko na wasan, yayin da ‘yan wasan na Benin suka mamaye wasan, bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

A kuma ranar Talata ‘yan wasan na Super Eagles za su kara da Crocodiles na kasar Lesotho a filin wasa na Teslim Balogun da ke Legas.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG