Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Jihohin Arewa Maso Gabas Su Na Shirin Zuwa Arafat


Wani al-Haji yana addu'a a kan Jabal al-Noor (dutsen haske) wanda ke bayangarin birnin Makkatul Mukarrama

Hukumomin Jihar Yobe sun ce sun shirya ma alhazansu abubuwa da yawa, yayin da na Jihar Gombe ma suka ce ba su fuskantar wata matsala

Mahajjata daga jihohin arewa maso gabashin Najeriya, wadanda suke kwana yau a Mina, su na shirin tashi da asubahin nan mai zuwa, tare da sauran alhazan Najeriya da na kasashen duniya dake aikin Hajjin bana, zuwa Arafat, domin zuwa Arafat.

Mahajjatan zasu yini a nan Arafat, domin gudanar da ibada a nan inda Annabi muhammad (saw) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, kafin su wuce zuwa Muzdalifa a bayan faduwar rana.

Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Injiniya Ibrahim Usman, ya ce a karon farko, dukkan alhazan jihar sun samu zuwa Madinah kafin su taho Makka don damarar fara aikin Hajjin. Haka kuma yace gwamnatin jiharsu ta taimakawa dukkan mahajjatan da kudin sayen ragunan layya.

Su ma alhazai daga Jihar Gombe, sun yaba da irin shirye-shiryen da hukumar alhazan jihar ta yi musu a nan Kasa Mai Tsarki. Wakliliyarmu Sa'adatu Mohammed Fawu da ta tattauna da su, ta ce alhazan sun gama hallara a Mina, kuma da asuba zasu doshi Arafat.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG