Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Najeriya Sun Fara Shirin Dawowa Gida


A halin da ake ciki Alhazan sun fara shirye shiryen dawowa gida bayan kamala aiki Hajji, ana sa ran kashin farko na Alhazan zasu iso Najeriya, yau Litinin bayan kamala aikin Hajjin bana.

Sakataren hukumar Alhazan jahar Bauchi, Alhaji Sulaiman Aliyu, ya ce mutun daya ne aka ya rasu daga jahar sa kuma mutane biyar da har yanzu ba’a gansu ba.

Daga jahar Gombe, kuwa an samu kimanin mutane tara da suka da suka samu raunuka sa’ilin na kuma akwai kimanin mutane biyar da ake nema,in ji Usman Gurama sakataren hukumar Alhazan na jahar Gombe, amma ya ce ba za’a yanke hukuncin cewa suna cikin wadanda suka mutu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:15 0:00

XS
SM
MD
LG