Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 5 Ne Suka Bata Yan Jihar Niger A Kasar Saudiyya.


Daga cikin mutane biyar din har da babban akanta na jihar Alhaji Shehu K Mohammed da kuma dan kwamitin aikin Hajjin da gwamnatin jihar Niger ta kafa Barister Isah Abubakar.

Babban sakataren jin dadin Alhazan na jihar Sheik Musa Ibrahim yace kawo yanzu suna ci gaba da neman wadannan mutane kamar yadda ya shaidawa wakilin sashen Hausa Mustafa Nasir Batsari ta wayan tafi da gidan ka.

‘’Dayaya daga cikin amirul hajji shine Barister Isah Abubakar muna cikin bincike har yanzu ba a tabbatar da al’amarin sa ba ana ci gaba da bincike, amma dai har yanzu ba aganshi ba tare da akanta janar na jihar ta Niger, cikin Alhazai ukkunda ake nema ba a gansu ba, su hudu ne amma kafin mu baro mina daya yazo ya same mu’’

A halin da ake ciki dai jamaa da dama a cikin jihar suna cikin halin damuwa da rashin sanin tabbas akan yan uwan su dake can kasar ta Saudiyya a sakamakon rashin samun cikakken bayani.

Ga Mustafa Nasir Batsari da ci gaban rahoton ‘’2 51’’

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

XS
SM
MD
LG