A kashi na biyu na tattaunawar da aka yi a taron da Muryar Amurka ta shirya a ofishin da ke Abuja, mahalarta sun bayyana matsalolin da suke gani sune sanadin sace yara da suka hada da rashin isassu da kuma makarantu masu inganci, sakacin iyaye, rashin gaskiya tsakanin al'umma, da kuma sakacin gwamnati.
Ku saurari tattaunawar da ta hada kan masu ruwa da tsaki da suka hada da jami'an tsaro, limaman addini, 'yan gwaggwarmaya, matasa, kungiyoyin sa kai da dai sauransu.
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.