Wadansu 'iyaye a Kaurar Namoda, jihar zamfara, sun yi zargin cewa, wani dan shekaru talatin ya yi wa karamar 'yarsu 'yar kasa da shekaru uku fyade. Suka kuma tabbatar da cewa, da farko hukumomi sun kama mutumin amma daga baya aka sake shi, ba tare da yi masu wani bayani ba. Suka kuma ce bisa ga dukan alamu hukumomi na neman yin watsi da batun.
Saurari bayanin da mahaifiyar yarinyar ta yi wa shirin Domin Iyali
Facebook Forum