Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya: Mutum 257 Sun Mutu a Hadarin Jirgin Sama


Jirgin Aljeriya da ya yi hatsari

Wani jirgin sojin Aljeriya mai dauke da sojoji ya fadi a yau Laraba, inda ya kashe mutum akalla 257, a cewar Ma’aikatar Tsaron Aljeriyar.

Hukumomi sun ce jirgin ya fadi ne kusa da karamin filin jirgin saman Boufarik, kimanin kilomita 25 daga kudu maso yammacin Algiers, babban birnin kasar, jim kadan bayan tashin shi.

Wadanda suka mutu sun hada da fasinjoji 247 da ma’aikatan jirgin guda 10.Yawancin wadanda suka mutu sojoji ne da ‘yan uwansu.

An kai gawarwakin asibitin sojoji na garin Ain Naddja don a tantance su, inji Ma’aikatar tsaron kasar.

Ma’aikatar tsaron ta kara da cewa jirgin yana da niyyar zuwa garin Tindouf ne da ke kudu maso gabashin Aljeriya.

Har yanzu dai ba’a san dalilin faduwar jirgin ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG