Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Saliyo: An Rantsar Da Shugaba Bio; Wilson Ya Ce Zai Ruga Kotu


Rantsar da sabon Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio
Rantsar da sabon Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio

Sakamakon zagaye na biyu na zaben Saliyo ya bar baya da kura. Yayin rantsar da wanda ya yi nasara, wanda ya sha kaye ya ce zai ruga kotu saboda ba a yi gaskiya ba.

Dan takarar da ya fadi a zaben Shugaban kasar Saliyo, y ace zai kalubalancin sakamakon a kotu.

Tsohun Ministan Harkokin Wajen Saliyo Samara Wilson ya bayar da sanarwar shirin kalubalantar sakamakon zaben jiya Alhamis, bayan da hukumar zabe ta ayyana Julius Maada a matsayin wanda ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben, wanda aka gudanar makon a karshen makon jiya.

Sakamakon da aka bayyana a hukumance ya nuna Maada Bio, dan takarar jam’iayyar adawa ta Sierra Leone People Party, ya ci kashi 52% na kuri’un. Shi kuma Kamara ya sami wajen kashi 48%.

Kamara, wanda dan takarar jam’iyya mai mulki ne ta All People’s Congress Party, ya fadi a wani jawabin da aka yada ta gidan talaijin cewa sakamakon zaben, “bai zo daidai da abin da masu kada kuri’a ke so ba” kuma jam’iyya APC za ta ruga kotu.

Amma yayin hidimar rantsar da shi, Maada Bio na cike da fara’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG