Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljeriya Na Kokarin Yin Kwaskwarima Ga Kundin Tsarin Mulkin Kasar


Louisa Hanoune, second left, Leader of Algeria's Workers' Party attends the constitutional reforms vote session in Algiers, Algeria, Feb. 7, 2016.

Gwamnatin Aljeriya ta yi jerin tarurrukan yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima game da takaita wa’adin mulkin shugaban kasa da karawa ‘yan majalisu karfi, to sai dai ‘yan adawa suna kokwanton ko zaben zai iya kawo wani canji mai ma’ana.

Zaben ya sami tsallakewa da kuri’un ‘yan majalisa kimanin 499, a yayin da guda 16 suka zura idanu ba tare da zaben ba, wasu ‘yan majalisar da dama kuwa kauracewa zaben raba gardamar suka yi.

Kwaskwarimar ta haifar da wa’adin mulki biyu sau biyu ga shugaban kasa, wanda gyara ne akan kwaskwarimar shekarar 2008, da ta ba Shugaba Abdulaziz Bauteflika damar sake tsayawa takarar wasu wa’adin mulki har sau biyu.

Haka kuma Shugaban kasar ne zai bada sunan Firaminista daga mafiya rinjaye a Majalisa. ‘Yan adawa sun ce kwaskwarimar ta kunshi abubuwa masu ma’ana. Amma sun ce ana bukatar sake kwaskwarima don takaita karfin ikon jam’iyyar Shugaba Abdulaziz ta FLN mai mulkin kasar.

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG