Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin Wasu ‘Yan Nijar Game Da Zaben Kasar


Tambarin Kasar Jamhuriyar Nijar

A ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu ne z a gudanar da zabukan gama gari a Jahuriyar Nijar, inda shugaba mai ci Muhammadu Isufu zai fafata da ‘yan takara 14.

A karshen makon da ya gabata ne aka kaddamar da yakin nema zabe bayan da hukumar zaben kasar ta CENI ta kusan kammala raba katunan zabe.

Shugaba Isufu a lokacin yakin neman zaben da ya fara a makon da ya gabata, ya ce tun a zagayen farko zai yi nasara.

Amma ‘yan adawa sun ce zancen na shi bagu ne kawai na siyasa domin a cewarsu ba zai kai labari ba.

Za a dai a je zagayen na biyu a zaben idan har ba a samu dan takara da ya samun yawan kuri’un da ake bukata ba.

Ga kadan daga cikin ra’ayoyin ‘yan kasar kan wannan zabe da ke tunkarar kasar kamar yadda wakilin Muryar Amurka Yusuf Abdullahi tattaro mana daga birnin Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG