Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifin Janar Buratai Ya Rasu


Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai Da Mahaifinsa, Alhaji Yusuf Buratai

Alhaji Yusuf Buratai, tsohon soja kuma mahaifin babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai, ya rasu yana da shekaru 106 da 'ya'ya 15 a raye kuma an yi jana'izarsa yau a Maiduguri da jami'an gwamnatin Borno da na gwamnatin tarayya suka samu halarta

Allah ya yiwa Alhaji Yusuf Buratai, mahaifin Janara Yusuf Tukur Buratai, rasuwa a asibitin koyaswa na Jami'ar Maiduguri bayan wata 'yar gajeruwar rashin lafiya .

An yi jana'izar mahaifin babban hafsan sojojin Najeriya din ne yau inda manyan jami'an gwamnatin tarayya da na jihohi suka kasance.

Alhaji Yusuf Buratai, wanda shi ma tsohon soja ne, ya rasu yana da shekaru 106 ya kuma haifi 'ya'ya fiye da 20. Guda 15 yanzu suna raye. Goma cikinsu mata ne. Guda biyar kuma maza ne cikinsu har da babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai.

Jana'izar ta samu halartar gwamnan Borno Kashim Shettima da kwamishanoninsa da 'yan majalisu da shugabannin riko na kananan hukumomi da kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas da sauran manyan jami'an soja dake aiki a jihar.

A bangaren gwamnatin tarayya mai ba shugaban kasa shawara a harkokin tsaro Janar Baba Gana Monguno mai ritaya ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayyan zuwa jana'izar. Tawagar ta hada da ministan tsaron kasa Mansur Dan Ali da Ministan ayyuka da gidaje, Alhaji Baba Shihori da Babban hafsan sojin sama, Sadique Abubakar da dai sauransu.

Haruna Dauda na da karin bayani a rahotonsa

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG