Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Allah Ya yiwa Saneta Gyang Pwajok Rasuwa


GNS Pwajok, tsohon saneta kum san takarar jam'iyar PDP a jihar Plato, Nigeria

Rahotannin daga jihar Plateau na nuni da cewa, Allah ya yiwa dan takarar gwamnan jihar karkashin jam’iyar PDP Saneta Gyang Nyom Shok Pwajok rasuwa.

Tsohon sanetan wanda aka fi sani da GNS Pwajok ya rasu ne a kasar Indiya bayan jinyar kwana biyu.. Mai Magana da yawun mamacin a lokacin takararsa, Chuwang Dung ya tabbatarwa wakiliyarmu Zainab Babaji rasuwar tsohon dan takaran gwamnan.

GNS Pwajok dai ya jima yana fama da laulayi, bisa ga rahotannin, ya fara rashin lafiyan ne lokacin yana takara, amma ya ci gaba da yakin neman zabe a cikin wannan yanayin. Daga baya aka daina ganinsa a bainin jama’a kafin a kaishi India inda ya cika.

A cikin makon nan ne dai, kotun dake sauraron kararrakin zabe a jihar Plato ta yanke hukumci kan karar da jam’iyarsa ta PDP ta kai tana kalubalantar zaben gwamna Simon Lalong. Kotun dai tayi fatali da karar ta kuma ayyana gwamna mai ci a matsayin wanda ya lashe zaben.

GNS Pwajok dai ya taka rawa a matakai dabam dabam a siyasar jihar Plato da ya hada da wakiltar tsakiyar jihar Plato, yayi aiki a matsayin babban jami’in gudanarwa a ofishin gwamna, kuma ana bayyana shi a matsayin matashi mai kwazo da hada kan al’mma.

Ga Bayanin Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG