Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'umma Na Kin Yarda Da Tuban Wasu 'Yan Boko Haram


Sojoji na atisayin yadda za su ceto mutane daga hanun yan ta'adda.

Wani bincike da Cibiyar Bunkasa Demokradiya ta yi ya nuna sakacin mahukunta akan kawo karshen yaki da 'yan ta'addar Boko Haram.

Ana cigaba da neman hanyoyin warware yaki da kungiyar ta’addar Boko Haram da ke chanza salon yaki da addabar arewa maso gabashin Najeria. Cibiyar Bunkasa Dimokradiya (CDD) ta hada wani taron hadin giuwar kungiyoyin farar hular Nijar da Najeriya, domin Muhawara akan rahotanin binciken da wasu cibiyoyin nazarin cigaban al’umma suka gudanar a Najeriya kan matsalolin da suka biyo bayan rikicin Boko Haram.

Ferfesa Jibiril Ibrahim na Kugiyar CDD ya bayyana cewa irin kashe kashen da ake yi a Najeriya abin mamaki ne, inda mafi yawancin wuraren da rikici ya barke wa, mafi yawancin shuwagabanin garuruwan sun gudu sun bar garin a lokacin da ake ta rikice rikice a garuruwan.

Jibril ya ce a Najeriya yanzu akwai yara milliyan sha uku waddanda basa zuwa makaranta suna almajiranci irin wanda ya sabawa yadda aka yi da, inda ake tura yaro ya je ya koyi Al’kurani maimaikon neman kudi da malamai ke tura su a yanzu. Jibril ya ce a ckiin irin waddannan yaran ne Boko Haram ke dauka, su mayar da su mayaka.

Binciken da Kungiyar CDD ta yi ya nuna cewa akwai sakacin mahukunta wajen ilimantarwa akan tanadin yaki da 'yan ta'adda. Wani lauya mai zaman kansa da ya halarci taron, Rilwana AbdurRahaman, ya ce abinda ya hana kawo karshen wannan rikici na Boko Haram shine rashin yarda damahukunta suke nunawa, da kuma zargin cewa sun kashe mutanen dake zuwa suna tsegunta musu inda 'yan Boko Haram suke.

Ga cikakken bayanin yadda ta kaya a wannan taron a bakin Sule Mummuni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG