Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar kudancin Sudan suna buki nuna murna da sakamakon zaben raba gardama


Al'ummar kudancin Sudan suna nuna farin cikinsu da jin sakamakon zaben raba gardama da hukumar zabe ta sanar yau.

Sakamakon farko na zaben raba gardama na nuni da cewa akasarin wadanda suka kada kuri'a sun zabi ballewa daga arewaci.

Jami’an gudanar da zaben raba gardama na kudancin Sudan sun ce sakamakon farko na zaben yana nuni da cewa akasarin wadanda suka kada kuri’a sun zabi ballewa daga arewaci a kuri’ar da aka kada farkon wannan watan. Adadin da aka buga a yanar gizon hukumar zaben ya nuna dukan kuri’un da aka kada a kudanci da kuma arewacin Sudan, inda kusan kashi casa'in da tara bisa dari na wadanda suka kada kuri’a suka zabi ballewa. Yau Lahadi aka sanar da sakamakon zaben karon farko a bainin jama’a a wani buki da aka yi a Juba babban birnin kudancin Sudan da ya sami halartar shugaban kudancin Salva Kiir. Ana kyautata zaton fidda cikakken sakamakon zaben ranar sha hudu ga watan gobe na Fabrairu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG