Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Nahiyar Turai Na Daukan Kungiyar IS A Matsayin Babbar Barazana Garesu


Harin Belgium

Rahoton wata cibiyar bincike mai suna Pew Research Centre, ya ce al’umar nahiyar turai na daukan kungiyar IS a matsayin babbar barazana ga kasashensu.

Sannan sai canjin yanayi wanda ya zo na biyu a jerin ababan da al’umar nahiyar ke ganin suna masu barazana, yayin da dumbin ‘yan gudun hijra daga Iraqi da Syria ke kwarara zuwa nahiyar a cewar binciken, wanda aka mai taken “Al’umar nahiyar Turai Na Fuskantar Duniya a Rarrabe.”

Bincike har ila yau ya nuna cewa, kashi 17 cikin 100 a kasashen turai goma da aka yi nazarin a kansu, sun nuna cewa kungiyar ta IS tana masu barazana kadan, yayin da kashi uku cikin dari suka nuna cewa kungiyar ba ta barazana ga kasashensu ko kadan.

Hare-haren da aka kai a Paris da Brussels a shekarar da ta gabata, sun sa batun ta’addanci a gaba-gaba a jerin ababan nuna damuwa ga ‘yan nahiyar ta turai, lamarin da ya sa aka kara tsaurara matakana tsaro.

Sai dai mafi yawan ‘yan nahiyar ta turai ba su amince a kara kudaden da ake kashewa ba a fannin soji, saboda a ganinsu daukan matakan soji zai iya kara haifar da kiyayya da tarzoma.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG