Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al’ummomin jihar Kebbi sun hada hannu a yunkurin yaki da cutar shan inna


Ana ba wasu maganin cutar shan inna

Kimanin masu aikin sa kai maitan daga kauyuka dabam dabam na jihar Kebbi sun hada hannu domin gudanar da ayyukan rigakafin shan inna

Kimanin masu aikin sa kai maitan daga kauyuka dabam dabam na jihar Kebbi ne suka hada hannu domin gudanar da ayyukan rigakafin shan inna, a kauyukan da aka fi samun kananan yara duke da cutar.

Masu aikin sa kan, suna shiga gida-gida, suna digawa kananan yara maganin rigakafin bayan samun horaswa a wani shirin da ake kira “change agents”. Banda nawayar aiwatar da shirin rigakafin da aka dorawa wadannan jami’an, zasu kuma rika ilimantarwa da wayar da kan al’umma a kan muhimman abubuwan da zasu taimaki rayuwrsu ta yau da kullum.

Masu aikin jinkan suna kuma wayar da kan iyalai dangane da cutuka kamar gudawa, da matakan shawo kan kamuwa da zazzabin cizon sauro da muhimmancin shayar da jarirai da nonon uwa.

Tuni jami’an suka fara gano kananan yaran da ba a yiwa rigakafi ba, wadanda suke cikin hadarin kamuwa da cutar, wadanda ake kyautata zaton a wannan karon, salon da aka dauka zai taimaka wajen samun hadin kai da goyon bayan iyaye wadanda a lokutan baya suke ki a yiwa ‘ya’yansu rigakafi.

Jihar Kebbi dai tana daya daga cikin jihohin da ake fama da yaduwar cutar shan inna a Najeriya. Duk da yake a halin yanzu ba a sake samun wani yaro da ya kamu da kwayar cutar ba, a shekara ta dubu biyu da goma sha daya, an sami kananan yara guda takwas dauke da cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG