Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyan Ruwa Yayi Barna a Kudancin Kasar Amurka


Irin barnar da ambaliyan ruwa yayi
Irin barnar da ambaliyan ruwa yayi

Wata mummunar guguwa da ruwan sama ya ratsa wasu jihohi a kudancin Amurka

Kimanin mutane 14 ne suka mutu sakamakon mummunar guguwa da ruwan sama da ya ratsa ta Jihohin dake kudancin Amurka wadanda suka hada da Texas, da Arkansas da Missouri da kuma Mississippi.

Gabashin Texas nan ne al’amarin yafi muni inda jerin guguwa ta kashe mutane kusan 4 ta kuma bar mummunar barna a baya a cewar Jami’ai.

Jami’ai sun ce mutane shida ne suka mutu a makwafciyar Jihar Texas wato Arkansas.

Irin barnar da muguwar guguwa tayi a jihar Texas
Irin barnar da muguwar guguwa tayi a jihar Texas

Wata mata ‘yar shekara 65 ta rasa ranta yayin da bishiya ta fado mata aka a DeWitt, Arkansas, kamar yadda jami’an ‘yansanda suka ce. A yankin Springdale kuwa wata yarinya ‘yar shekara 10 ce ta mutu sakamakon ruwa da yayi awon gaba da ita.

‘Yansanda na cigaba da neman yara biyu da suka bata wadanda ake kyautata zaton suna cikin mota ruwa yayi awon gaba dasu.

Jami’an da ke kula da manyan hanyoyi a Missouri sunce wata mata yar shekara 72 ta nitse a ruwa duk da kokarin da mijinta yayi na cetonta a yayin da ambaliyar ruwa tayi awon gaba da motarsu a ranar Asabar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG