Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa: An Gargadi Jihohin Najeriya Da Su Zauna Cikin Shiri


Wani yankin jihar Bayelsa da ambaliyar ruwa ta mamaye a Najeriya, ranar 6 ga watan Oktoba 2012.

Zuba shara da yin gini a magudan ruwa na daga cikin ababan da masana muhalli suka ce na haifar da ambaliyar ruwa, lamarin da ya sa wasu jihohi a Najeriya suka dukufa wajen daukan matakan kare aukuwar bala'in.

Hukumomin Najeriya na kira ga gwamnatocin jihohi da su tashi haikan wajen wayar da kan al’umominsu domin kaucewa aukuwar ambaliyar ruwa a yankunansu.

Wannan kira na zuwa ne bayan gargadi da aka yi na cewa akalla jihohi 30 da kananan hukumomi 30 ake fargabar za su fuskanci ambaliyar ruwa a bana.

A baya-bayan nan jihohin Naija da Legas sun yi fama da ambaliyar ruwa lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Wannan gargadi ya sa hukumomin jihar Gombe wacce ke arewa maso gabashin Najeriya, suka tashi tsaye wajen fadakar da al’umar jihar kan matakan da za su iya dauka domin kaucewa ambaliyar ruwan.

“Tsabtace muhalli abu ne da ya tattari aikin kowa da kowa, ba na mutum daya ba ne.” In ji gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo

Ya kuma kara da cewa kasancewar jihar Gombe mai dauke da rairayi da kuma kasancewa tana cikin kurmi akwai bukatar mutane su yi hattara.

“Barazana irin wannan a ko da yaushe muna fuskantar ta.” In ji Dankwambo.

Kwamishinar kula da muhalli ta jihar Gomben Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha ta ce, “muna nan tsaye ba dare ba rana…. Muna kira a ko da yaushe cewa magudanan ruwa da aka yi ba wajen zuba shara ba ne.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG