Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa da Ruwan Sama a Kasar Girka Sun Hallaka Mutane 15


Mandra, Megara and Nea Peramos, a Girka su ne wuraren da ambaliyar ruwa ya yi barna
Mandra, Megara and Nea Peramos, a Girka su ne wuraren da ambaliyar ruwa ya yi barna

Ambaliyar ruwa da ruwan sama kamar da baki kwarya sun kashe mutane 15 a garuruwa daban daban irinsu Mandra da Megara da dai sauransu

Ambaliyar ruwa a sassa dabam-dabam da ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa a kasar Girka, ta hallaka mutane 15 a wasu kauyuka uku da ke yammacin Athens babban birnin kasar jiya Laraba.

Garuruwan Mandra da Nea da Peramos da Megara, wurare ne da aka sansu da yawan kamfanoni da wurare gine-ginen adana abubuwa musamman a bayan gari.

Jami’ai sun kwatanta ambaliyar da ta auku cikin dare da kwararowar ruwa daga wata mabubbugar da ke kan tsaunukan yammacin yankin Attica.

“Wannan al’amari ne mai matukar wahalarwa; Mabubbugar Niagara ta malalo kuma babu mai iya tsai da ita,” inji Mataimakin Gwamnan yankin, Yiannis Vassileiou ga gidan talabijin na gwamnati ERT.

Magajin Garin yankin ya bayyana ambaliyar da cewa ita ta fi muni cikin shekaru 20 da su ka gabata.

“An yi hasarar komai. Wannan bala’in shigin wadanda su ka faru ne tun a zamanin Annabawa,” a cewar Magajin Garin Mandara Ioanna Kriekouki ga ERT.

Firaministan Girka Alexis Tsipras ya ayyana rana guda ta makoki a duk fadin kasar, sannan ya bayyana goyon baya ga iyalan wadanda abin ya rutsa da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG