Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa: Mutum Uku Sun Hallaka a Jihar Nassarawa


Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa.
Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa.

Jihar Nasarawa ta fara fuskantar barnar ruwa yayinda hukumomi ke fadakar da al’umma kan barazanar da ambaliya ka iya haddasawa a wassu jihohin Najeriya.

Al’ummar unguwar kofar kaura dake cikin garin Lafia, a gabar wani kogi sun shaida cewa, tuni ambaliyar ta hallaka rayuka uku yayinda kayayyaki da dama suka salwanta.

A cikin hira da Muryar Amurka, mazauna yankin sun bayyana cewa galibinsu talakawa ne, wadanda basu da halin sake gina wani matsuguni, suka kuma nuna irin hadarin dake tattare da ci gaba da zama a wurin da suka ce tamkar zama a bakin ramin mutuwa ne, suka kuma nemi taimakon gaggawa daga gwamnati da suka bukaci ta saye gidajen ta samar masu wani matsuguni.

Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa
Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa

A nashi bayanin gwamnan jahar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, babban abinda ya ke kawo ambaliyar ruwa a wurare da dama shi ne yawan zubar da shara a magudanun ruwa da ke toshe hanyar ruwa. Ya kuma sanar da sake dawo da tsarin yin shara kowanne karshen wata don yashe magudanan ruwa.

yankunan-jihohin-adamawa-da-taraba-sun-fara-fuskantar-ambaliyar-ruwa

hukumomi-sun-yi-kashedi-a-kan-ambaliya-a-kano-da-makwabtanta-

A nata bangaren, hukumar agajin gaggawa NEMA a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya, wadda alhakin kula da wadanda irin wannan bala’in ya aukawa ya rayata a wuyanta ta bayyana cewa, banda agazawa wadanda lamarin ya shafa, suna fadakar da al’umma kan matakan kare kai daga ambaliyar.

Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa
Ambaliyar ruwa a jihar Nassarawa

Ko a cikin watan Satumba, an fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a jihar Kogi sakamakon gocewar da tekun Naija ya yi, wanda ya kwashe gonaki da gidajen daruruwan mutane, ya kuma tafi da motoci da dama da ke tafiya kan hanya.

Hukumomi da kwararru sun yi gargadi da cewa akwai yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a jihohi da dama na Najeriya da kuma wadansu sassan kasashen Afrika.

Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji cikin sauti.

Ambaliyar Ruwa: Mutane Uku Sun Hallaka a Jihar Nassarawa:3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG