Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane 42 A Jamhuriyar Nijer


Ambaliyar ruwan sama
Ambaliyar ruwan sama

Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta bayyana cewa ambaliyar ruwa ta haddasa rugujewar dubban gidaje yayin da mutane da dama su ka hallaka a kasar sakamakon ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a watan Augustan da ya gabata.

A taron manema labaran da ya kira ministan Ayyukan Jinkai Alhaji Lawan Magaji ya bayyana cewa ruwan sama ya haddasa barna a dukkan jihohin kasar ta Nijer, koda yake a bana matsalar na da sauki idan aka kwatanta da halin da ake ciki bara warhaka.

Rashin mutunta ka’idar gini da nuna halin ko in kula a kan batun mutunta hakkin makwabtaka na daga cikin manyan dalilan da suka janyo wannan barna. Alhaji Lawan Magaji ya bada alkaluman asarar da ambaliyar ruwan sama ta janyo, ciki har da mutane 42 da suka rasa rayukansu.

Tuni dai gwamnatin ta fara tallafa wa wadanda wannan bala’i ya afka wa da dan abin masarufi inji ministan. Ya ce an rigada an fara bada gudunmuwar kayan abinci da tabarmi da sauran kayan taimako ga mutane dubu saba’in da ambaliyar ta shafa.

Kawo yanzu kashi talatin cikin dari na tallafin da ake bukata ne ya shigo hannun hukumomi sanadiyyar jan kafar da ake fuskanta daga abokan hulda yayin da a yanzu haka kogin Isa ko Niger ke kara batsewar da ke barazana ga mazauna gabarsa, kuma Ma’aikatar Hasashen Yanayi ta yi gargadin cewa akwai yiyuwar samun saukar ruwan sama mai yawa a watan nan na Satumba.

Daga birnin Yamai ga rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG