Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Tsunami Ta Hallaka Mutane 222 a Indonesiya


Wasu wuraren da ambaliyar tsunami ta shafa a Indonesiya
Wasu wuraren da ambaliyar tsunami ta shafa a Indonesiya

Kasar Indonesiya, wadda kwanan baya ta yi fama da girgizar kasa, ta sake fuskantar wani bala'i bayan da ambaliyar tsunami ta malale tare kuma da yin mummunar barna da hallaka mutane a yankin gaba.

Wata ambaliyar tsunami ta malale wuraren shakatawar bakin ruwa da ke mashigar ruwa ta Sunda a kasar Indonesia da daren jiya Asabar agogon yankin.

Mai magana da yawun Hukumar Kai Daukin Gaggawa ta Indonesia, Sutopo Nugroho, ya ce, "Mutane wajen 222 ne su ka mutu, baya ga wasu 843 da su ka ji raunuka da kuma wasu 28 da su ka bace."

Ita kuma kungiyar Red Cross shiyyar Indonesia cewa ta yi a wata takardar bayani, "da yiwuwar adadin wadanda abin ya rutsa da su ya karu yayin da ake cigaba da tattara alkaluma."

Barnar ta fi aukuwa ne a yankuna uku: wato da Kudancin Lampung da ke Sumatra da Serang da kuma Pandegland na Java, wanda ke yammacin Jakarta, babban birnin kasar - wadanda duk ke wuraren mashigar ta Sunda. a cewar Nugroho.

Haka zalika daruruwan gidaje da otal-otal wajen 9 da kuma kananan jiragen ruwa wajen 350 ne ambaliyar ta lalata, a cewar hukumar kai daukin gaggawar kasar ta Indonesia.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG