Accessibility links

Amfani da gidajen sauro ya rage mace-mace ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro


Wasu suna hada raga mai hana sauro

Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoto cewa, an sami raguwar mutuwar al’umma ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro

Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoto cewa, an sami raguwar mutuwar al’umma ta dalilin kamuwa da zazzabin cizon sauro, tsakanin ‘yan gudun hijira dake kan iyakar kasar Sudan.

A lokutan baya, zazzabin cizon sauro ne yake kashe ‘yan gudun hijirar kasar Sudan fiye da kowacce cuta. Sai dai a halin yanzu, duk da yake zazzabin har yanzu yana kisa, rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa, zazzabin cizon sauro ya kasance cuta ta biyar dake kisan ‘yan gudun hijirar.

An samu raguwar kisan da cutar ke yi ne, sakamakon wani shiri da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da ake kira Ba Komi Banda gidan sauro, “Nothing But Nets” gamgamin yaki da cutar zazzabin cizon sauro mafi girma da aka gudanar a duniya da ake kyautata zaton zai taimaka wajen kawo karshen mace mace sakamakon kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro kafin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Shirin ya kaddamar da wata gidauniyar gagagawa da nufin aikawa da gidajen sauro dubu goma domin ceton rayukan ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da suke kauracewa kan iyaka da ake fama da tashin hankali

XS
SM
MD
LG