Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aminu Amanawa: Tsige Nyako Rikici Ne


RA'AYOYINKU - Aminu Amanawa
RA'AYOYINKU - Aminu Amanawa

A Yau Inaso Inyi Tsokaci Kan Danbarwar rikicin siyasa, dake Ruruwa a Jihar Adamawa, Tsakanin Gwamnan Jahar Murtal Nyako da Mataimakinsa, da kuma Majalissar dokokin Jahar.

Wanda wannan Ko shakka babu yana kara tabbatar mana da cewa, akwai lauje cikin Nadi, kan Yunkurin da Majalissar Jahar Keyi Na Tsige Gwaman Jahar da mataimakinsa.

Wanda abun lura anan Shine Shekera nawa Gwamna Nyako da mataimakinsa suka shafe suna Jagorantar Jahar Batare da Majalissar Jahar Sunyi yunkurin tsigesa ba sai a yanzu?

A saboda Haka 'Yan Majalissun Jahar Adamawa, yakamata Ku dawo daga Rakkiyar taki gona, idan har Masu gidan Rana a ka baku dan ku tsige Gwamna Nyako da Mataimakinsa.

Doman Wannan Ba abun da zai Haifarwa Jahar, Face Ruruwar rikicin Siyasa, Wanda kuma Zai kai Jahar ga koma baya a Har kar cigaban Jahar.

Daga Karshe Nake Addu'ar Allah Ya Kawo Mana Karshen Mulkin danniya, da zalunci a najeriya, Amin.

--------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

Sakonni da Masu Amfani da Shafi Suka Aiko

Muryar Amurka da Shafukan yanar Gizo masu dauke da bayanai, na iya barin masu anfani da kafar su rubuta ra’ayoyinsu su saka abubuwan da suka rubuta su yi sharhi, su aika da sakonni da hotuna da zane-zane da saka labarai da ma ire-irensu a matsayin bayanai da masu amfani suka aiko. To sai dai ka amince cewa duk abun da ka rubuta zai bi namu hanyar sadarwa ko wasu da muke muamala da su, su yi a madadinmu da yanar gizo. Ka amince cewa Muryar Amurka da kafar Sadarwa ta Yanar Gizo kafofi ne na anfanin jama’a ba hanyoyin sadarwar mallakar wasu ba ne.

Kana iya aiko da bayanai kamar wato abubuwan da ka rubuta wa Murya Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo wadanda mallakarka ne, wato kai ne ka rubuta, ko kuma kana da izinin marubucin ka yadasu ta yanar gizo. Ba zaka karya dokar da ta hana satar abun da wani ya rubuta ba ko ka hana wani hakkin gudunmawarsa game da rubutun wanda ya hada da ikon mallaka kamar sunan da wani ya yi rajista dashi domin aikin ko tambari da yake anfani da shi. Haka ma ba zaka saci asirin sana’arsa ba ko na kansa ko na talla. Ka yarda kuma ka tabbatar kai ne kake da iko da kuma izinin yin anfani ko yada ayyukan kuma ka baiwa Muryar Amurka izinin yada abun da ka rubuta.

Ka adana duk wata shaidar mallaka da kake da ita bisa ga duk ayyukan daka sa a Muryar Amurka da kafar Sadarwar Yanar Gizo. Amma domin ka baiwa Muryar Amurka da Kafar Sadarwa ta Yanar Gizo, to ka baiwa VOA ikon mallaka ita kadai na har abada ba tare da biyan wani haraji ba. Kuma zata yi anfani da shi duk fadin duniya, ta iya kofa, ko ta baiwa wani ko ta yi masa ‘yar kwaskwarima a yi anfani da shi a bainar jama’a da yin anfani da shi ta wasu hanyoyi daban daban.

XS
SM
MD
LG