Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Amsoshin Jega Game Da Zaben Najeriya


Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Attahiru Jega yayi taron tattaunawa da manema labarai a Abuja inda ya amsa tambayoyin manema labarai daban-daban.

A hirar ta Farfesa Jega da ‘yan jarida ya fara da amsa tambaya game da maganar zaben jihar Rivers sai yace, “Da safen nan na sami wasikar daga jam’iyyar APC ta bukatar a soke zabe a Jihar Rivers, amma muna binciken maganar”. Haka kuma da aka masa maganar tsinkayen da yakewa makomar zaben sai ya bada amsa da cewa, “Muna fatan zaben nan zai ci kai ga gaci bisa da’a da doka kamar yadda yake gudana”.

Haka kuma Jega ya godewa ‘yan Najeriya da cewa, “Hukumar zaben ta yaba da juriyar da ‘yan Najeria suka nuna da fahimtar wahalhalun da suke cikin lamarin”. Ya kara da cewa, “INEC tana yaba yadda al’ummar Najeriya suka fito yin zabe cikin kwanciyar hankali”. Jega ya sake cewa, “Sannan abin farin ciki ne yadda na’urorin zaben suka yi aiki a mafi yawan rumfunan zabe”.

Da aka tambayi Farfesan game da jefa kuri’ar ‘yan gudun hijira sai ya kada baki yace, “Hukumar zabe ta gabatar da zabe a sansanin ‘yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeria”. Hatta maganar na’urorin da suka ki aiki a wasu mazabun sai ya amsa tambayar da cewa, “Ana ci gaba da binciken dalilan da suka hana wasu na’urorin tantancewar aiki”.

Ya kara da cewa, “A sakamakon matsalolin wasu na’urorin, zaben bai samu gamuwa a jiya ba har ya kawo zuwa yau”. Ya amsa tambayar yadda zaben kr guda da cewa, “Bisa rahotannin da muke samu daga wasu ofisoshinmu na wasu jihohi, ana ci gaba da tattara sakamakon zabe kuma abin yana tafiya sumul”. Ya kuma ce, “Ba karamin abin farin ciki ba ne yadda zaben ya gudana cikin nasara duk da tangardar da ke faruwa a kasar”.

Game da matsalar tsaro a wasu jihohin sai ya amsa da, “Bisa matsalolin tsaro da aka samu a wasu jihohin a jiya da ana zaben ne yasa aka kaucewa zaben kamar yadda hukumar ta karbi rahoton abin”. Ya amsa tambayar da ke neman sanin wanda ke da alhakin fadar sakamakon zabe da cewa, “Hukumar INEC ce kadai doka ta yarda ta fadi sakamakon zabe, sannan laifi ne wani ya yiwa hukumar riga malam masallaci ya fadi abinda hukumar ta tattaro na sakamakon zabe”.

Jega bai bar maganar cewa wasu da shekarunsu bai kai ba sun yi zabe, inda yace, “Mun sami rahoton wadanda shekarunsu bai kai ba a Taraba sun yi zabe, don haka mun umarci a bayyana mana jami’in zaben wajen”. Ya kara da cewa, “Barin wanda shekarunsu bai kai ba su yi zabe laifi ne a doka. Sannan zamu bincika mu kuma dauki mataki”. Ya kuma tabbatar da cewa, “Idan bincikenmu ya nuna cewa ma’aikacinmu yana da hannu a aikata laifuffukan zabe, to ba makawa zamu ladabtar da shi bisa doka”.

Farfesa Jega ya rufe da tambayar lattin kayan zabe inda yace, “Matsalolin da akan samu na jinkirin kai kayan zabe wasu wurare saboda matsalar abin hawa, to zamu yi kokari mu ga mun maganceta”. Har yanzu dai 'yan Najeriya suna nan sun kasa kunnuwan jin wadanda zasu lashe zabubbukansu ciki har da na shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG