Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMSOSHIN TAMBAYOYINKU IV *Wadanne kasashe ne matasa suka Samu damar kama madafun mulki? * kuma ko matasan sun taka rawar gani?


Ibrahim K Garba
Ibrahim K Garba

Masu sauraronmu assalama alaikum; barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.

Yau za a ji kashi na hudu kuma na karshe na amsar tambayar na mai cewa:

  1. Wai Don Allah a wadanne kasashe ne matasa suka Samu damar kama madafun mulki?

2. kuma ko matasan sun taka rawar gani a zamanin mulkin nasu?

Wassalam ku huta lafiya.”

Mai tambaya: Dalhatu manjos Gobir, Samaru Busstop Zaria, Jahar Kaduna, Najeriya.

To idan mai tambayar, Malam Dalhatu Manjos Gobir, da ma sauran masu saurare na tare da mu, zan zakuda gefe, wakilin Muryar Amurka a Kaduna, Isa Lawan Ikara, ya gabatar ma ku da kashi na karshen na amsar da ya samo daga Mataimakin Furfesan Tarihi, wanda zai dora daga inda ya ke bayani kan yadda matashin Shugaban Kasar Koriya Ta Arewa, Kim Jung Un, ya tsara yadda zai ciyar da kasarsa gaba, ta wajen sake fasalin sojojin kasarsa.

To sai a kasance da mu makon gobe don jin amsoshin wasu tambayoyin. Yanzu a madadin wanda ya amsa ma na tambayoyin: Mataimakin Furfesa, Salisu Bala, da wakilan Muryar Amurka Isa Lawan Ikara, da wanda ya hada ma na sautin, Hailu Haile, da Injiniyanmu, ni Ibrahim Ka-Almasih Garba ke cewa sai makon goben idan Allah ya kai mu. Wassalam.

Saurari cikakken shirin:

07-23-22 AMSOSHIN Tambayoyinku .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:02 0:00
XS
SM
MD
LG