Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta yi Tayin Tukuicin Milyan 30 kan Shugabannin al-Sahaba.


Hotuna daga ma'aikatar tsaron Netherlands gameda mafasa cikin teku daga Somalia.

Amirka tayi tayin bada tukuicin dala miliyan talatin da hudu ga duk wanda ya bata bayanin inda shugabanin Al Qaida da aka danganta da kungiyar Al Shabab ta Somaliya suke.

Amirka tayi tayin bada tukuicin dala miliyan talatin da hudu ga duk wanda ya bata bayanin inda shugabanin Al Qaida da aka danganta da kungiyar Al Shabab ta Somaliya suke.

Alhamis ma’aikatar harkokin wajen Amirka ta bada wannan sanarwar, karkashin shirin bada tukuci domin ayi adalci. Wannan ne karon farko da za’a kebe yan kungiyar Al Shabab musamman.

Amirka ta yi tayin bada tukucin dala miliyan bakwai domin samun bayanin inda wanda ya kafa kungiyar Al Shabab yake, sa’anan kuma ta yi tayin bada tukucin dala miliyan biyar domin samun bayana inda mukarraban shugaban kungiyar Al Shabab na kut da kutu su hudu suke.

Haka kuma, Amirka ta yi tayin bada tukucin dala miliyan uku domin samu bayanin inda wasu manyan shugabanin kungiyar su biyu suke.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG