Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta fitar da wasu sabbin manufofi kan yadda za ta rika hulda da kasashen Afirka.
Amurka ta ce ya zama dole bukatunta, su zamanto abu mafi muhimmanci a dangatakarta da Nahiyar ta Afirka.
A yau Alhamis, mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkar tsaro, John Bolton, ya bayyana wadannan manufofi a nan birnin Washington DC.
Bolton ya kara da cewa, za a rika gudanar da huldar kasuwanci tsakanin Amurka da kasashen Afirka, ta yadda bangarorin biyu za su amfana.
A cewar Bolton daga yanzu, Amurkan ba za ta rika ba kasashen Nahiyar ta Afirka tallafi barkatai ba, sannan ba za ta kara daukan nauyin wani aikin soji na wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ba ya haifar da wani abin alheri ba.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 10, 2023
Trump Ya Sami Goyon Bayan Manyan 'Yan Republican
-
Yuni 06, 2023
NIJAR: Yawan Matan Da Ke Mutuwa A Yayin Nakuda Ya Ragu.
Facebook Forum