Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Bernie Sanders Ya Fara Goya Wa Joe Biden Baya


Bernie Sanders da Joe Biden

Sanatan jihar Vermont, Bernie Sanders ya bai wa abokin karawarsa tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden goyon baya a hukumance, a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba, inda za a buga da shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican.

Hakan na faruwa ne jim kadan bayan da Bernie Sanders ya janye daga nema zama dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Democrats.

“Dole mu mayar da Trump shugaban kasa na wa’adi daya, muna bukatarka a fadar White House,” abin da Sanders ya fada wa Biden kenan a wani taron hadin gwiwa da suka bayyana ta yanar gizo.

“Zan yi duk abin da zan iya naga hakan ta faru, Joe” Sanders ya yi alkwarin haka.

Shi kuma Biden ya mayar da martini da cewa “ina son na gode maka kan wannan, babban lamari ne kuma bani goyon baya abu ne mai muhimmanci a gare ni."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG