Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Rasha Zasu Tattauna Domin Kaucewa Fitina Tsakaninsu A Syria.


Amurkawa 'yan asalin Syria suke zanga zangar saboda shigar da Rasha tayi a rikicin kasar ta sham.

Amurka da Rasha zasu koma teburin shawarwari da zummar kaucewa hadari a sararin samnaiyar Syria, yayinda kasashen biyu suke kai hare haren bama-bamai daban daban a yankin.

Kakakin maikatar tsaron Amurka Peter Cook ya fada jiya jumma'a cewa za'a fara tattaunawa zagaye na biyu cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Amurka wacce take adawa da goyon bayan da Moscow take baiwa shugaban Syria Bashar al-Assad, tace ba zata hada kai da Rasha ba, amma ta amince ta tattauna kan matakai na tabbatar da lafiya da kaucewa hadura a sararin samaniya.

Jiragen yakin Rasha sun keta sararin samaniyar Turkiyya cikin kwanaki da suka wuce, wanda ya janyo hukumomin kasar suka bayyana rashin amincewarsu, har kungiyar tsaro ta NATO ta sha alwashin zata kare kawayenta. Haka nan wani jirgin yakin Rasha yazo dab da jirgin yakin Amurka d a bashi da matuki.

A cikin makon nan Moscow ta harba makamai masu linzami daga jiragen ruwanta da suke tekun da ake kira Caspian, Amurka tana zargin hudu daga cikin makaman sun fada a Iran. Moscow ta musanta cewa babu wani makami mai linzaminta da ya baude.

Da alamun shawarwari da za'a gudanar zasu fi maida hankali kan tazarar da jiragen yakin kasashen biyu ya kamata su baiwa juna, da kuma harshen da matuka jiragen zasu yi amfani dashi wajen tuntubar juna.

Labarin wannan shawarwari yana zuwa ne a dai dai lokacinda Amurka ta bada sanarwar canza salon gudanar da shirin horasda 'yan tawayen Syria da basu kayan aiki domin su yaki kungiyar ISIS, shirin wanda aka ware dala milyan $500 ma'aikatar tsaron Amurka take kula da shi.

Shirin zai sauya daga tantance 'yan tawaye masu sassaucin ra'ayi da kuma horasda da su a kasashen Jordan, da Saudi Arabaia, da Qatar, da kuma a hadaddiyar daular Larabawa.

Maimakon haka, shirin zai samarda goyon baya da jiragen yaki da horaswa ga shugabannin kungiyoyin 'yan tawaye, kamar yadda jami'an fadar white House suka bayyana.

XS
SM
MD
LG