Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Birtaniya Sun Yiwa Rasha Kashedi Kan Harin Kutsen Naurorin Kwamfutocinsu


Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha
Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha

A wani abun da aba'a saba gani ba kasashen Amurka da Birtaniya sun yiwa Rasha kashedi akan yiwa kwamfutocinsu kutsen da ya shafi kamfanoni da wasu ma'aikatun gwamnatocinsu

A halinda ake ciki kuma, Amurka da Birtaniya sun fitar da kashedi na ba sabam ba a jiya Litinin, dake zargin Rasha da zafafa kai harin kutsen na’urar kwammfuta a kan kamfanonin Amurka da Birtaniya da ma’aikatun gwamnati da kuma wasu abeban more rayuwa.


Amurka da Birtaniya sun ce wannan hari na gamagari a fadin duniya tun a shekarar 2015 ne Rasha ta fara shi, kuma tana iya zafafa shi zuwa wani mizani na mummunar hari.


Ma’aikatar harkokin tsaron cikin gida da ta binciken manyan laifuka a nan Amurka ta FBI da kuma cibiyar kare hada-hada- ta internet ta Britaniya, sune suka bada fitar da wannan gargadin, kuma sanarwar ta kunshi bayanai kan irin matakai da kamfanoni za su dauka na kare kansu.


Jami’an Amurka da Birtaniya sun ce hare haren sun shafi kungiyoyi da ma’aikatu masu tarin yawa da suka hada da kamfanonin samar da internet, da kamfanonin masu zaman kansu, da kuma muhimman kampanonin samarda muhimman kayan more rayuwa. Sai dai kasashen biyu basu ambaci sunayen wadanda kutsen suka yiwa illa, da cikaken bayanai kan irin barnar da hakan ya janyo.


Jami’an na Birtaniya da Amurka sun ce sun yi imanin cewa fadar Krimlin ta shugaban Rasha ce ta bada umarnin akai hare haren.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG