Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Brazil Sun Bude Sabon Shafin Dangantaka


Bayan wasu shekaru da dama, yanzu haka kasar Brazil da Amurka sun bude wani sabon shafi na hulda tsakanin kasashen biyu mafiya girma a yammacin duniya.

Shugabannin Amurka da Brazil, kasashe biyu mafiya girma a yammacin duniya, sun yi alkawarin inganta huldar cinakayya, da hadin kai ta fuskar soji, ta yadda har ma Shugaban Amurka Donald Trump ke nuna cewa ya kamata Brazil ta shiga kungiyar Kawance ta NATO.

Trump ya ce, amma kafin hakan ya yiwu, sai ya tattauna da mutane da dama.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Shugaban Brazil Jair Bolsonaro, Shugaban na Amurka ya kuma yi alkawarin cewa Amurka za ta goyi bayan shigar Brazil kungiyar kasashe 36 na habbaka tattalin arziki ta (OECD), wadda ta kunshi har ma kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Da ya ke jawabi a harshen Portugal, Shugaba Bolsonaro na Brazil, ya ce wannan ziyarar da ya kawo ta bude sabon babi a huldar Brazil da Amurka, ya kara da cewa zabensa da aka yi kwanan nan, ya sa kasar ta Brazil ta samu Shugaban kasa wanda bai gaba da Amurka, wanda rabon hakan ya faru tun tsawon shekaru gommai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG